Samar Da Tsaro Ba Aikin Gwamnati Kaɗai Bane – Honorabul Kuraye

Ɗan Majalisa mai wakiltar ƙaramar Hukumar Charanchi a majalisar dokokin Jihar Katsina Honorabul Lawal Isah Kuraye, ya bayyana cewar yana da matuƙar muhimmanci jama’a su gane cewar aikin samar da tsaro a ƙasa ba aikin gwamnati bane ita kadai, aikine wanda ya rataya a wuyan jama’a kowa da kowa.

Lawal Kuraye ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu kan bikin ranar dimukuraɗiyya a Kaduna.

Ɗan majalisar ya kara da cewar an baro shiri tun rani ne sakamakon yadda aka yi watsi da Sarakunan gargajiya akan harkar tsaro aka koma rayuwa kara zube, wanda hakan ya bada gudunmawa wajen lalata tsaro a ƙasa.

Kuraye ya tabbatar da cewar Sarakuna sune suke da sani da masaniya akan kowa dake yankin su, babu mai shiga ko mai fita face da sanin su, amma a yanzu duk an manta hakan dole muga ba daidai ba.

Dangane da bikin ranar dimukuraɗiyya da ke gudana kuwa Lawal Kuraye yace a magana ta gaskiya Shugaban ƙasa Buhari ya yi rawar gani a sha’anin shugabanci idan aka kwatanta da baya, sai dai wasu matsalolin da ba a rasa ba waɗanda ke damun duniya baki ɗaya.

Hakazalika ɗan Majalisar ya kuma yaba gami da jinjina ga Gwamnan jihar Katsina Aminu Masar wanda ya bayyana shi a matsayin maceci wanda burin shi shine yadda zai ceto Jihar Katsina daga matsalolin da gwamnatocin baya na PDP suka tsunduma ta ciki.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.