Mahadi Murucin Kan Dutse Kashi Na 2

A rubutu na da ya gabata na yi bayani akan tabbacin da nake dashi na cewar fafutukar da Mahadi Shehu yake yi ba domin kanshi yake yi ba, yana yi ne domin al’ummar Jihar Katsina, Alhamdulilah a yanzu dai kam gaskiya ta yi halinta kowa ya gane haka.

Ga dukkanin wani ɗan Jihar Katsina mai kishin Jihar ya sani kuma ya gamsu mulkin Jihar Katsina a hannun Gwamna Aminu Masari Jihar ta shiga cikin wani mummunan yanayi mai sanya firgici da takaici, duba da yadda komai a Jihar ya durkushe, Katsinawa suka kasance tamkar bayi a kasar su.

Zan bada misali da harkar ilimi a Jihar Katsina, Jihar Katsina wadda a baya can zamanin mulkin Gwamna ‘Yar’aduwa da Shema take sahun gaba ta fuskar ilimin zamani a bangaren Arewa, an wayi gari a yanzu jihar tana ajin baya, duk da irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnatin Masari ke hanƙoron kashewa ta fannin.

A Hotuna da Mahadi Shehu ya rinƙa fitarwa wanda ke nuni da irin yadda gine-ginen makarantu a jihar Katsina suka yi muguwar lalacewa, da yadda Mahadi ke bayyana sunan kowace Makaranta da yankin ƙaramar Hukumar da take, ya sanya muka bibiyi maganar domin gano gaskiyar lamarin, kuma Allah cikin ikon shi a ƙananan Hukumomin da muka ziyarta abin da muka gani sai dai muce Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un!!!.

Idan muka waiwayi bangaren tsaro kuwa zamu iya cewa anan ne gizo ke sakar, domin irin mahaukatan kuɗaɗe da gwamnatin Masari ke fitarwa tana kashe mu raba a tsakanin mukarraban Gwamnati karkashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar Mustapha Inuwa abin ba a magana, Jihar Katsina ta shiga cikin wani irin mawuyacin hali na farmakin kuraye! Jihar ta gangara cikin wani rami sai abin da hali ya yi.

Fallasa asirin da wannan Bawan Allah Mahadi Shehu ke yi ma wadannan Shugabanni maciya amana, shine dalilin da ya sanya suka kulla gaba dashi da ƙoƙarin ganin bayan shi.

Allah muke roko da ya kara tsare wannan bawa nashi Mahadi Shehu daga sharrin masharranta ya bashi jajircewa wajen fallasa gaskiya komai dacinta Allahumma Amin.

Sai mun hadu a rubutuna na gaba da yardar Allah.

Aminu Ismail ‘Yar’aduwa Dalibi ne a Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’aduwa sashin koyon aikin Jarida.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.