Gwamnatin Buhari Ta Faɗi Warwas A Fuskar Tsaro – Jakadan Hayin Banki

An bayyana cewar lalacewar harkar tsaro a karkashin mulkin Shugaban kasa Buhari ya rufe dukkanin wasu ayyuka na cigaba da gwamnatin za ta iya hanƙoron samu domin rayukan jama’a sune gaba da komai.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kaduna Alhaji Abdullahi Gambo Abba, lokacin da yake tsokaci dangane da kewayowar ranar Dimukuraɗiyya 12 ga watan Yuni a tattaunawar shi da wakilinmu a Kaduna.

Gambo ya kara da cewa ko shakka babu gwamnatin tarayya ƙarkashin jagorancin Buhari ta yi rawar gani wajen gudanar da wasu aikace-aikace da ƙoƙarin inganta rayuwar al’umma, amma kalubalen tsaro da ya kara lalacewa a mulkin ya zamana ba za’a ga wadancan cigaba ba sai koma baya muraran.

Ɗan siyasar wanda a hannun guda yake rike da Sarautar gargajiya ta Jakadan Hayin Banki Kaduna, ya soki lamirin iyalan marigayi Abiola wadanda ke korafin cewa su ba su amfana da komai ba a sauya ranar dimukuraɗiyya da akayi daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, inda ya tunatar dasu cewar hikimar sauya ranar domin a tuna da tarihin tsabtataccen zaɓe da aka yi ne inda ‘yan Najeriya suka yi zaɓe ba tare da banbancin ƙabila ko yanki ba.

Galibin ‘yan Najeriya musamman Arewa suka zaɓi Abiola suka yi watsi da Bashir Tofa, kuma akayi zaben babu banbancin addini domin Abiola da mataimakin shi Kingibe dukkanin su musulmai ne kuma aka zabe su babu korafi, wannan ne sila sauya ranar dimukuraɗiyya amma ba wani abu na daban ba.

Daga karshe Abdullahi Gambo Abba ya nemi gwamnatin Buhari da ta ƙara zage damtse wajen shawo kan matsalar tsaro dake addabar kasar fiye da lokutan baya.

Leave a comment

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.