June 12: Gamayyar Kungiyoyin Arewa Sun Nesanta Kansu Daga Shiga Zanga-Zanga

Gamayyar kungiyoyin Arewa sun fito fili sun nesanta kansu daga shiga wata Zanga-Zanga da wasu ke shirin aiwatarwa a ranar 12 ga watan Yuni, wato sabuwar ranar dimukuraɗiyya.

Mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Abdul-Azeez Sulaiman ne ya bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwa da suka fitar, inda ya bayyana cewar baya cikin tsarin gamayyar kungiyoyin Arewaci shiga cikin duk wata sabga ba batare da fahimtar inda aka sa gaba ba.

Sanarwar ta bayyana cewar ko kaɗan gamayyar kungiyoyin ba zasu taba shigar da yankin Arewa cikin wata harka da mai sarkakiya wadda basu da masaniya cikinta ba.

Gamayyar kungiyoyin sun ce babban burin su shine janye Arewa daga cikin tarkon da kungiyar tsagerun Inyamurai ke dashi na shirya Zanga-Zanga wacce daga baya za ta rikide zuwa wani yanayi na tashin hankali musanman a yankin Arewa.

“Mun dade da gano manufar miyagun kungiyoyin Kudancin Najeriya wadanda suke da wani mummunan buri na haifar da rikici da tashin hankali a Jihohin Arewa da sunan Zanga-Zanga”.

Gamayyar kungiyoyin sun kara da cewar wani dalilin da ya sanya ba za su shiga cikin wannan Zanga-Zangar ba shine tun asali su basu yarda da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar dimukuraɗiyya ba, ballantana har su aiwatar da wani abu da sunan ranar ba.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.