A Kyale Inyamurai Su Kafa Kasar Biyafira – Ƙungiyoyin Arewa

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya sun yi kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Buhari da cewar cikin gaggawa ya bada dama ga Inyamurai su kafa kasar da suke ta hanƙoro akai ta Biyafira domin zaman lafiyar Najeriya.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin Abdul-Azeez Sulaiman kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Kungiyoyin Arewan sun cigaba da cewar tuni ba tun yau ba suka bayyana matsayin nasu na a amince Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira domin bayin Allan ‘yan Arewa su samu natsuwa da kwanciyar hankali daga farmakin da tsagerun Inyamurai ke kai musu a yankin Kudancin Najeriya.

Dangane da martanin da shugaban kasa ya mayar wa tsagerun na cewa zai yi maganin su nan bada dadewa ba, kungiyoyin Arewan sun ce kalaman Buhari akan wannan matsala abin takaici ne da ke nuna gazawa da raunin gwamnatin shi a fili.

“Ba tsoro ko fargaba bane ‘yan Arewa ke yi na kasar nan ta rabe, sai dai kawai natsalar da ake fuskanta a har kullum shine ɓangaren manyanmu da ke ta kalaman ayi hakuri a zauna ƙasa guda, wanda hakan ne ya haifar mana da raini har sashin Kudanci ke mana kallon ba a bakin komai muke ba suke barazanar a raba ƙasa, wanda kowa ya san wanda zai ji jiki idan aka rabar ƙasar”.

Saboda haka ya kamata shugabannin mu su gane cewar hanya guda ta kaucewa barkewar yaƙin basasa a Najeriya shine abar Inyamurai su kafa kasar tasu ta Biyafira.

Kungiyoyin sun yi kira ga jama’ar Arewa da su zauna lafiya su kwantar hankalin su, sannan su goyi bayan Inyamurai su yi gaba su bar mana Najeriya su tafi Biyafirar su.

Sannan mun zuba ido mu ga matakin da shugaban kasa zai dauka nan da kwanaki 30 domin kawo karshen tataburzar da Kungiyoyin Inyamurai suke haddasawa a kasar nan a kusan kullum.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.