Makarantar Imamu Malik Ta Karrama Asiya Ganduje Da Lambar Girmamawa

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-An Karramata Ne Kan Ƙoƙarinta Na Hidimtawa Addinin Musulunci Da Kuma Taimakon Marayu Da Marasa Ƙarfi.

Yau Laraba, 27 ga watan Nobemba, 2019.
A taron da ta gudanar a jiya Talata domin saukar karatun Alqur’ani na yara guda (105), makarantar (Imamu Malik Bin Anas Littahfizil Qur’an Wattajweed) wacce ke Unguwar Sabon Gandu a ƙaramar Hukumar Kumbotso, ta karrama ƴar mai girma gwamnan Jihar Kano, Hajiya, Asiya Balaraba Ganduje, (Fulani Zanan Laisu Fika), “Ƴar Aljannah”, da gagarumar lambar yabo ta girmamawa da jinjina.

Kamar yadda hukumar makarantar ta bayyana tunda farko a takardar albishir da ta aike mata, sun “karrama ta ne kan ƙoƙarin da ta ke na yi wa addinin Allah (Musulunci) hidima da kishi da kuma yadda ta ke jajircewa wajen taimakon marayu da marasa ƙarfi a cikin al’umma”.

Taron wanda ya samu halartar muhimman mutane kama daga kan shehunan malamai da alarammomi da sarakunan gargajiya da ƴan siyasa waɗanda su ka haɗa da mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero da mai girma Sanata, Sardaunan Kano Mallam Ibrahim Shekarau da mai girma kwamishinan ayyuka na musamman, Dakta Mukhtar Ishaq Yakasai da kuma shugaban ƙaramar Hukumar ta Kumbotso, Onarabul Ado Fanshekara da sauran manyan baƙi da dama.

Mai martaba Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne ya miƙa lambar yabon ga uwar marayu, Hajiya Asiya Balaraba Ganduje (Fulani Zanan Laisu Fiƙa), “ƴar Aljannah” a madadin hukumar gudanarwa ta makarantar.

Hajiya Balaraba Ganduje ta basu kyautar Shadda ga ko wanne na miji, atamfa ga ko wacce ɗaliba mace. Malamai Maza 20 suma sun samu kyautar shadda ga ko wannen su.

Ko a ƴan kwanakin da su ka gabata, uwar marayun, Hajiya Asiya Balaraba Ganduje, “ƴar Aljannah”, (Fulanin Zanan Laisu Fiƙa), ta samu lambobin yabo da dama waɗanda aka karrama ta da su dangane da ƙoƙarin da ta ke kan ayyukan jin ƙai da taimakon al’umma.

Sannan kuma har kamfanin mai na ƙasa (NNPC) shi ma ya karrama ta da gagarumar lambar yabo kan nasarar lashe gasa da ta yi a matakin ƙasa gaba ɗaya.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.