Sharhin Siyasar Duniya Jiya Da Yau Domin Ma’abota Nazari (6)

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

-Tasirin Sabbin Kafafen Sadarwa Na Zamani (New Media) Wajen Kawo Sauyi A Siyasar Duniya A Cikin Ƙarni Na (21).

-Rawar Da Sabbin Kafafen Sadarwar Zamani (Social Media) Su Ka Taka Wajen Samar Da Sauyi Kan Siyasar Afrika A Ƙasashen Tunusiya, Masar, da Libiya.

A cikin shirin da ya gabata, na taɓo tarihin rayuwar: Winston Churchill, wani fitaccen marubuci, babban jami’in rundunar soji, shugaba a rundunar sojin ƙasar Birtaniya, ɗan siyasa, ɗan gwagwarmaya, wanda kuma ya taka gagarumar rawa wajen samun galaba a kan ƴan Nazi na ƙasar Jamus a yaƙin Duniya na biyu, wato (World War II).

Yau Lahadi, 17 ga watan Nobemba, 2019.
A cikin shirin na yau kuma, zan taɓo batun sabbin kafafen sadarwa ne na zamani (Social Media) da kuma tasirin da su ke da shi wajen samar da sauyi da cigaba a siyasar Duniya gaba ɗaya a wannan ƙarni da mu ke ciki na ashirin da ɗaya, (21).

Fasahar sadarwar zamani a yau a iya cewa wata masarrafa ce da ke sarrafa Duniya cikin jagorantar al’amuran rayuwa na al’umma ta kuma taimaka wajen haifar musu da sauye-sauyen cigaban rayuwa mai ma’ana da ɗorewa. A wannan ƙarni na (21), fasahar zamani ta mamaye dukkan rukuni da sassan rayuwar ɗan adam.

Yau a duniya, babu wani wuri da ɗan adam zai boye, duba da yadda ake da fasahar (GPRS) wacce ta ke gano wurare, hatta al’amuran yaƙe-yaƙe yau a duniya ana sarrafawa tare da amfani da fasahohin sadarwa na zamani a kuma samu nasara da galaba kan abokan gaba.

Ba shakka yau duniya ta zama ta zamani ta na tattare a tafin hannu, wacce kuma fasahar sadarwar zamani ita ce tushen wannan nasara da aka samu. Ba wai iya sadar da saƙo kaɗai ko sauƙaƙa zirga-zirga kawai ta ke yi ba, ta taimaka matuƙa wajen jawo nesa kusa ga al’umma ta hanyar amfani da na’urar tauraron ɗan adam da na’ura mai ƙwaƙwalwa ta yadda duk nisan wurin fasahar kan jawo shi ya dawo kusa ba tare da wata tangarɗa ba.

Fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa ta taimaka matuƙa wajen rage nisa a tsakanin ƙasashe da nahiyoyi ta yadda cikin ƙasa da minti ɗaya ta hayar latsa www, za ta haɗo dukkan wani bayanai da ɗan adam ke buƙata tare da sabbin kafafen sadarwa na zamani (New Media).

Ƙarni na (21) ya zo da gagarumin cigaba kan amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen sadarwa da kuma yaɗa bayanai da jawabai a duniya gaba ɗaya.

Yanar gizo-gizo ta zamto tana mafi ƙarfi da tasiri wajen ba da dama ga al’umma matasa maza da mata a duk duniya su yi amfani da wayoyinsu na hannu wajen nemo bayanai da sadar da saƙo a rubuce da yaɗa hotuna da bidiyo a YouTube da sauran dandalukan shafukan sada zumunta.

Ta hayar yanar gizo-gizo, bayanai su kan watsu su kuma barbazu a duk duniya cikin ƙanƙanin lokaci tare da bayyana halin da ake ciki a kowane lokaci, yau duniya ta zamto a dunƙule ta haɗa jama’a kusa da kusa da juna. Yau a duniya Jama’a su kan yi amfani da sabbin kafafen sadarwa na zamani wajen ƙalubalantar dukkan wata gwamnati mai salon mulkin kama karya ko neman wani haƙƙi nasu a hannun mahukunta cikin ruwan sanyi ta hanyar rubuce-rubuce ko kuma ta hanyar yin amfani da kafofin wajen shirya zanga-zanga da ma tarzoma a wasu lokutan.

Sabbin kafafen sadarwa na zamani su kan taimaka wajen sanin haƙiƙanin matsaloli da tunanin zukutan al’umma ta yadda jama’a kan bayyana ra’ayoyi da manufofinsu ba tare da wata shakka ko wata fargaba ba a kowane lokaci a kuma kan komai.

Me Ake Nufi Da Sabbin Kafafen Sadarwa Na Zamani (Social Media),

Kafar sadarwar zamani, ko kuma sabbin kafafen yaɗa labarai na zamani ko kuma kafafen sada zumunta da abota da kuma tafka muhawawa, (Social Media), sabuwar fasaha ce ko sabbin kafofi ne ko hanyoyi ne na sadarwa waɗanda su ka samu a sanadiyyar cigaban zamani. Inda jama’ su ke hawa su bayyana ra’ayinsu da hangensu da ƙwarewarsu da tananinsu. Ta hanyar wallafa rubutaccen saƙo ko na hotuna masu motsi (bidiyo) da marasa motsi (Images) ko kuma naɗaɗɗun bayanai ko zantuttuka (audio).

Sannan akwai sassa daban-daban ko kuma matattarar aika saƙonni da bayyana ra’ayi ko adana bayanai da muhimman zantuttuka na tarihi da ilimi da falsafa. Waɗanda duk su na ba wa al’umma damar shiga domin neman bayanai. Daga cikin waɗannan matattarar bayanai akwai (Wikipedia, Gather.com, YouTube, Digg, Flicker, Miniclip, Google, da sauransu, waɗanda dukkanninsu shafukane ko matattara da ake tara bayanai a cikinsu waɗanda masu ziyara su je ziyarta domin samun bayanai da hotuna da bidiyo har ma da wasanni.

Waɗannan ba su ne shafuka kaɗai ba, akwai shafuka irin su LinkedIn wanda shafi ne na ƙwararru da kuma shafuka irin su Facebook, Twitter, WhatsApp, Instgram waɗanda dukkaninsu shafuka ne da ake amfani da su wajen sadarwa yau a Duniya da kuma wasu shafukan da a baya an yi yayinsu sun wuce.

Rawar Da Sabbin Kafafen Sadarwar Zamani (Social Media) Su Ka Taka Wajen Samar Da Sauyi Kan Siyasar Afrika A Ƙasashen Tunusiya, Masar, da Libiya:

A Tarihin siyasa a Nahiyar Afrika, siyasa ce wacce ta yi ƙaurin suna wajen samun shugabannin ƙasashe masu mulkin kama karya da danne haƙƙin al’umma. Ta yadda a mafi yawan ƙasashe sai dai sojoji su yi juyin mulki inda ba a yi juyin mulki ba kuma shugabannin ƙasashen kan nema dauwama a kan mulki da maida ƙasashen ƙarƙashin bin tafarkin jam’iyyar siyasa ɗaya kawai.

Masu mulkin kama karya a nahiyar afrika su kan bi dukkan wasu hanyoyi da matakai wajen neman tabbata a kan mulki ciki kuwa har da ɗaukar matakan kawo sauyi da gyare-gyare kan kundin tsarin mulki wanda zai yi daidai da son zuciyoyinsu.

A ƙalla ƙasashe guda uku na Nahiyar Afrika sunyi yunƙurin yi wa kundin tsarin mulkin ƙasashensu kwaskwarima domin ya zo daidai da son zuciyoyinsu na cigaba da mulki har abada. Daga cikin ƙasashen akwai Libiya da Masar da kuma Tunusiya waɗanda shugabannin ƙasashen na wancan lokaci su ka nemi dauwama a bisa kan madafun iko har sai da jama’ar ƙasashen su ka taka musu birki.

Zamanin shugaban ƙasar Tunusiya, Zen Abidinal Bin Ali, ya kasance zamani matsananci wanda cin hanci da rashawa ya yi wa katutu ta yadda ta kai har ma al’ummar ƙasar sun fidda tsammani da samun wani sauƙi a zamaninsa su ka shiga zaman jiran samun sauyi.

Bin Ali ya ɗaiɗaita tattalin arziƙin wannan ƙasa, sannan rahoton tattalin arziƙi na Duniya ya tabbatar da kasancewar Tunusiya a matsayin ƙasa ta farko a nahiyar Afrika sannan ƙasa ta 32 a duniya cikin ƙasashe 139.

Sannan Bin Ali ya gaza shawo kan matsalar rashin aikin yi wacce ta yi ƙamari musamman a tsakankanin matasa da kuma kasa shawo kan matsalar talauci da fatara waɗanda su ka mamaye birni d karkara na ƙasar gaba ɗaya. Wanda kuma hakan ne ya haifar da tarnaƙi da tashe-tashen hankula.

Tayadda kuma jama’a su ka yi ta amfani da kafafen sadarwa na zamani irin su Facebook, WhatsApp da Youtube su na sanar da duniya halin da ake ciki. Tare da bayyana nuna adawarsu da kuma ƙin jinin gwamnatin. Inda su ka jagoranci fafutukar juyin juya hali.

Dokar ta ɓaci da shugaba Bin Ali ya sanya a ranar 14 ga watan Jannuware 2011 tare da alƙawarin gudanar da zaɓe cikin wata shida, ko kaɗan ba ta taimaka wajen kawo karshen halin tashin hankalin da ake ciki ba.

A kuma wannan dalili ne mulkin Bin Ali na tsawon shekaru 24 ya kawo ƙarshe. Wanda kuma kafafen sadarwa na zamani su ne su ka taka gagarumar rawar hamɓarar da gwamnatin Bin Ali, inda jaridar New York Times ta bayyana akasarin matasan ƙasar sun maida hankali ne kan amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen nuna adawarsu da gwamnatin da kuma shaidawa Duniya halin da ake ciki a lokacin gudanar da boren. Inda ƙididdiga ta tabbatar da cewar a wannan lokaci an sanya bidiyon boren sama da guda (30,000) a Youtube

A ranar 25 ga watan Jannuware 2011, sama da masu zanga-zanga mutum 90,000 ne su ka yi rijista da shafin Facebook inda su ke baza bayanai ga al’ummar ciki da wajen ƙasar Masar da su goyi bayan gangamin da su ke na adawa da gwamnatin Husni Mubarak wacce ta haifar da matsalolin rashin aikin yi da talauci da kuma cin hanci da rashawa.

Ta yadda har sai da ta kai mahukunta a ƙasar Masar sun nemi katse hanyoyin yanar gizo-gizo da kiran waya saboda taƙaita yaɗuwar bidiyo da hotuna da bayanan zanga-zangar da ake cigaba da yaɗawa a wannan lokaci. Amma duk da haka sai da al’ummar wannan ƙasa su ka yi nasarar hamɓarar da gwamnatin Mubarak a sanadiyyar amfani da kafofin sadarwar zamani New Media, inda Mubarak da kansa ya bayyana yin murabus ɗinsa ta bakin mataimakinsa Umar Suleman kamar yadda kafar watsa labarai ta New York Times ta bayyana a shekarar ta 2011.

Ƙarin misali kan ƙasashen Afrika da aka yi amfani da kafafen sadarwa na zamani wajen gudanar da juyin juya hali ita ce ƙasar Libiya, duk kuwa da cewar dakarun tsaron Gaddafi su na bibiyar bayanai da dukkan tattaunawar da ake ta hanyar waya salula amma duk da haka sai da masu juyin juya halin su ka samu galabar yin amfani da kafofin wajen shiryawa da kuma tsara zanga-zangar kifar da gwamnatin ta Gaddafi.

Wani masani ya bayyana cewa “daga hujjojin da mu ka yi la’akari da su, kafafen sadarwa na zamani sun zama wani tsani na samar da ƴanci da kyautata dimokaraɗiyya a yammacin Nahiyar Afrika da kuma Gabas ta tsakiya, tare kuma da haɓaka cigaban harkokin siyasa”.

Duk waɗannan ƙasashe guda uku, shugabannin da aka kifar da gwamnatinsu kamar yadda wasu masanan su ke faɗa, sun yi tanadi ne na gadar wa ƴaƴansu madafun iko. Shugabanni ne na mulkin kama karya waɗanda su ka nemi maida harkokin mulkin ƙasashen iya su da iyalansu kawai.

Misali, Mubarak ya tsara ɗansa mai suna Gamel zai gaje shi. Shi ma Bin Ali ya tsara ɗaya daga cikin zuriyarsa wani zai gaje shi. Haka shi ma Gaddafi a tanadinsa Seif Islam Gaddafi ɗansa na biyu shi ne zai gaje shi. Wannan dalili da sauran dalilai su ne su ka sanya su ka tarawa kansu maƙiya, su ka kuma yi amfani da (Social Media) wajen shirya zanga-zangar ganin bayan gwamnatocin nasu.

(Social Media) ta taka gagarumar rawa wajen kifar da gwamnatin a ƙasashen larabawa na Tinusiya da Masar da Kuma Libiya. Ta yadda hatta manyan mawallafa (Bloggers) a wancan lokaci duk sun karkata ne wajen wallafa bayanan juyin juya hali tayadda kuma hakan ya taimaka matuƙa wajen jawo hankalin duniya kan abubuwan da ke faruwa a ƙasashen har su ka samu nasarar kifar da waɗannan gwamnatoci.

Wannan kuma shi ne ya ke ƙara shaida mana yadda (Social Media) ta ke da ƙarfi da kuma tasiri a wannan zamani wajen kawo sauyi ga rayuwar al’umma ta fuskar tattalin arziƙi da siyasa da ma sauran al’amuran rayuwar yau da kullum da zamantakewa.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.