An Karrama Balaraba Ganduje Da Lambar Yabo Ta Gasar NNPC

DAGA Bashir Abdullahi El-bash

Yau Alhamis, 7 ga watan Nuwanba, 2019.
Ɗiyar mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, (Fulani Zanan Laisu Fika) ta samu nasarar samun matsayi na ɗaya a cikin wata gagarumar gasa da aka shirya a kamfanin mai na ƙasa (NNPC) a duk Nageriya a tsakanin maza da mata dattijai da matasa da matsakaita na kamfanin, amma ita ce ta yi nasarar lashe gasar gaba ɗaya.

A jiya Laraba, 6 ga watan Nobemba, 2019 shugaban rukunin kamfanin na (NNPC) Mallam Mele Kolo Kyari, wanda ya samu wakilcin babban jami’in gudanarwa na hukumar, Mallam Farouk Sa’id, shi ne ya miƙawa Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje (Fulani Zanan Laisu Fiƙa) lambar yabon a madadin kamfanin gaba ɗaya saboda wannan gagarumar nasara da ta samu.

Haƙiƙa wannan abin alfahari ne ga al’ummar Jihar Kano gaba ɗaya, duba da yadda ɗiyar mai girma gwamna ta samu wannan nasara a matakin ƙasa gaba ɗaya. Kuma duba da kaifin basira da hazaƙa da jajircewa irin na Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje (Fulani Zanan Laisu Fika) ko shakka babu fiye da wannan nasara ma za ta iya samu.

Kuma ɗumbin al’umma a wannan Jiha sun taya Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, (Fulani Zanan Laisu Fiƙa) murnar wannan nasara da ta samu. Tare da yi mata fatan Allah ya ƙara mata nasara a rayuwa ya kuma ƙara cigaba da ɗaukaka daraja da kimar Baba Ganduje da iyalansa a duk Duniya gaba ɗaya. Duba da kasancewarta babbar haziƙar mace mai ƙoƙarin taimakon al’umma a kowane lokaci kamar yadda Baba Ganduje ya ke yi.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.