Muna Kira Ga Izala Da Su Takawa Kabiru Gombe Birki – Tijjaniyah

Sakataren ‎ Kungiyar Tijjani ta duniya wanda ya kunshe jami’an Gwamnati da Yan Kasuwa ‎da Manoma da kuma almajirai Mohammed Garba Binkola ya nemi kungiyar Izala ta kwabI shaikh Kabiru Gombe akan irin kalamansa da tayi akan ba tun zabar Buhari.

A cewar Sakataren Tijjaniyar bai kamata Kabir Gombe wanda shi ne Sakataren Izala ta Kasa ya rika furta kalamai da nufin bata yan darikar Tijjaniyar ba.

Shaihin Malamin ya ce su yan Tijjaniya ba’asansu da neman tashin hankali ‎ba Dan haka sai ya bukaci shugabannin Yan Izala da su dauki mataki akan Sakataren masu ta hanyar kwabarsa.


‎” Mu masu dogaro ne da kanmu ba Dan wani ya sanmu ba. Muna kuma yin ikilasi domin Allah da kuma m‎a’aikin Manzon Allah.‎ Wannan furuci na Kabiru Gombe bai dace ba domin yanzu akwai muruden mu dake sama da ni su suka aikomin da wannan labari domin in gani in kuma ji abinda shi Kabiru Gomben ya ce.

“Sannan basu tsaya nan ba sai da suka bincike hasalin shi Kabiru Gombe. Ni ba girmana bane in tsaya ina mayar da martani akansa domin kowa na horuminsa ne.

“Koda akan Izala kawai aka ce ya yi magana bai da ce ya ce hakan ba a wannan lokaci da Shugaban kasa ya kirasu ya ce a zauna lafiya. Amma sai gashi ya tsallaki yana sukar Darikar Tijjaniya wanda a duk afirka Tijjaniya ce ta fara kafa daular Musulunci. . Shehu Umar Futi shi ya fara kafa daular musulunci a Kanfarjaro.

“7Shehu Usman Danfodio shi ya kafa tamu daular musulunci a Najeriya‎
A karkashin Kadiriyya. Sannan dansa Muhammed Bello ‎ sune jigajigan darikar Tijjani saboda haka daga ina mutum ya fito da zai ce zai suke yan Tijjaniya.

“Shugaban Kasa Buhari da kansa ya ce yasan cewa yawon daliben Shehu ibrahim inyas sun kai miliyan sittin a Najeriya saboda haka ba wayanda kake ganin suna zuwa Mauludi ne kawai yan Darika. Yayansi da matansu ba.‎

“Yan darikar yanzu ba irin na da bane da zaka rika batasu amma su yi shiru saboda malamansu dake nuna masu su yi hakuri a zauna lafiya. Yanzu in ka matsa masu sai su yi maka yawan kawura.. wannan nake ji masa tsaro kuma wannan Abu da ya fadi ba taimakon shugaba Buhari ya yi ba.

‎”Mu Buhari namu ne kuma mu ba yan siyasa bane saboda haka ko an fadi ko ba’a fadi ba muna tare da shi. Duk da yake shi Kabiru Gomben ya gyara maganarsa bayan an yi masa ca akwai bukatar a rika kiyaye kalamai.

“Dan haka wannan kalami nasa ya sa muke yin kira ga yan Izala da su tabbatar da sun ja hankalinsa da ya daina irin wayannan maganganu ko kuma su kwabe shi akan yin irin wayannan maganganu nasa. Domin babu wanda yasan yan darika da fitina saboda haka muke yin kira ga jama’armu da su kwantar da hankalinsa su cigaba da zama lafiya da kowa domin cigaban addini da kuma kasar mu baki dayanta.

Sent from my BlackBerry 10 smartphone.

Leave a Reply

Please log in using one of these methods to post your comment:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.